28 Disamba 2019 - 06:11
Turkiya Tana Shirin Aikewa Da Sojoji Zuwa Kasar Libya

Gwamnatin kasar Turkiya za ta bukaci majalisar dokokin kasar ta amince da aikewa da sojojinta zuwa kasar Libya a farkon watan Janairu mai kamawa.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Turkiya za ta bukaci majalisar dokokin kasar ta amince da aikewa da sojojinta zuwa kasar Libya a farkon watan Janairu mai kamawa.

Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ne ya bayyana hakan, bayan da gwamnatin kasar Libya da duniya ta amince da ita, ta bukaci taimako daga Turkiya.

Shugaban kasar ta Turkiya ya kara da cewa; Amincewa da aike sojojin zuwa kasar Libya shi ne aiki na farko da majalisar dokokin kasar za ta yi bayan ta koma hutu a ranar 7 ga watan Janairu.

Rajab Tayyib Urdogan ya kara da cewa; Za mu je in da aka gayyace mu, ba za mu je inda ba a kira mu ba.”

Gwamnatin Libya mai matsuguni a birnin Tripoli da ke karkashin Firai Minista Fayez Al-Sarraj, ta aike da bukata a yau Alhamis zuwa ga kasar Turkiya tana son da ta taimaka ma ta da sojoji a yakin da ta ke yi da Halifa Haftar.

Turkiya ta ce sojojin da za ta aike za su bayar da horo ne ga gwamantin ta Libya, amma ba za su shiga yaki ba.


/129